Rahoto daga Musa Yusuf Sanyinna
Mai shari’a Muhammad Sa’idu Sifawa na Babbar Kotun Jihar Sakkwato ya sami Labaran Aliyu da Abdulrahman Lawal da laifin zamba tare da yanke masu hukuncin ɗaurin shekaru biyu kowannensu a gidan yari. An yanke masu hukuncin ne a ranar Laraba, 11 ga Fabrairu, 2026 bayan sun amsa laifinsu kan tuhume-tuhume daban-daban guda ɗaya-ɗaya na zamba. Tuhumar da aka yi ma Aliyu ita ce ta damfarar mutane daban-daban a shekarar 2025 har Naira miliyan bakwai (N7,000,000) ta hanyar ce masu zai iya ninka kuɗi. Ya yi amfani da kuɗin ya sayo mota ƙirar Marsandi GLK mai lambar maɗaukinta WDCGG8HB5AF315979 wanda yin hakan ya saɓa ma sashe na 310 na dokar final kod ta zamba cikin aminci ta jihar Sakkwato, inda aka tuhunce shi dokar mai lamba 311. Shi kuma Abdulrahman Lawal an tuhumce shi da niyyar damfara inda a cikin shekarar ta 2025 ya karɓi Naira dubu ɗari da goma (₦110,000.00) ta hanyar yaudara ga mutane ba tare da sun sani ba da iƙirarin yana da ikon ninka kuɗi. Yin hakan ya saɓa ma sashe na 310 na final kod ta Jihar Sakkwato, kuma ana hukunta shi a ƙarƙashin Sashe na 311 na wannan doka. Bayan waɗanda ake tuhuma sun amsa laifinsu, lauyan gwamnati mai gabatar da ƙara, Aliyu Bokani Usman, ya roƙi kotu da ta yanke masu hukunci daidai da doka. Mai shari’a Muhammad Sa’idu Sifawa ya yanke wa Aliyu hukuncin daurin shekaru biyu tare da zaɓin biyan tarar Naira dubu ɗari (₦100,000.00). Haka kuma ta ba da umurnin ƙwace motar Marsandi GLK ɗin da aka saya da kuɗin laifi don a mayar wa wanɗanda aka cuta da kuɗaɗensu. Haka zalika, kotun ta yanke ma Lawal hukuncin ɗaurin shekaru biyu tare da zaɓin biyan tarar Naira dubu ɗari (₦100,000.00). An kuma ƙwace waya samfurin Samsung S10E da aka samu daga kuɗin laifi don a mayar ma gwamnati.
Hukumar EFCC ce ta gurfanar da su a gaban kotu bayan bincikenta ya nuna suna cikin wata ƙungiya da ake kira “Sai Mallam” da ke aiki a Sakkwato, wadda ta shahara wajen ruɗi da jan hankalin jama’a da sunan cewa su manyan bokaye ne masu iya ninka kuɗi da arzuta mutane. An bayyana cewa suna yaudarar mutane har daga ƙasashen Nijar da Kwad De-Buwa da Kamaru da Burkina Faso.






